Gwamnatin Zamfara ta rufe kafofin yada labarai 5 kan taron siyasa

0
47

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da rufe wasu kafofin yada labarai guda 5 saboda abinda ta kira saba ka’ida wajen yada labaran siyasa kwana guda bayan haramta harkokin siyasa a Jihar lamarin da danganta da matsalolin tsaro.

Kwamishinan yada labaran Jihar Ibrahim Dosara ya bayyana tashoshin da dokar ta shafa da suka hada da tashar talabijin na kasa NTA da tashar Pride FM mallakar Rediyo Najeriya da Gamji TV da Gamji FM da kuma Al’umma TV.

Taron PDP

Dosara yace wakilan wadannan tashoshi sun halarci taron Jam’iyyar PDP a Gusau inda aka samu arangama da kuma rasa rayukan mutum guda, bayan majalisar tsaro ta bada umurnin hana tarurrukan.

Kwamishinan yada labaran yace gwamnatin jihar Zamfara ta baiwa kwamishinan ‘Yan Sanda umurnin kama duk wani ma’aikacin wadannan tashoshi da yaje aiki bayan umurnin rufe su da gwamnati ta bayar.