Sojoji sun kashe ’yan boko haram 6 a Borno

0
102

Dakarun Bataliya ta 152 ta rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun yi nasarar kashe ’yan ta’addar Boko Haram 6 a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.

Kamar yadda wata majiya mai tushe ta sanar, an kashe maharan ne a ranar Lahadin da ta gabata a wani harin kwantan bauna da suka kai a kan hanyar Kumshe zuwa Banki a jihar ta Borno

Wani manazarcin yaki da ta’addanci kuma kwararre kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya tabbatar da harin.

Ya yi karin haske da cewa, sojojin sun yi kwanton bauna ne bayan wani rahoton sirri da suka samu cewa an ga wasu ’yan ta’addan Boko Haram da dama wadanda ake zargin sun sace wa matafiya da dama dukiyoyinsu a yankin.

Bayanai sun ce ayyukan sintiri da sojojin ke yi a kan hanyar na da alaka da wannan gagarumar nasara da sojoji suka samu.

Ana iya tuna cewa, a ranar 11 ga watan Oktoba, sojoji suka kashe ’yan ta’addan Boko Haram fiye da goma a hanyar Kumshe zuwa Banki.Sai dai da dama daga cikin ’yan ta’addan da suka tsira sun tsere garuruwan Ngauri da Gargash tare da manyan motocinsu da babura, inda suka kafa sansani da nufin kai hari daya daga cikin garuruwan Mayinti da Darajamal.

Zagazola ya tattaro rahoton cewa, Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta aika da wani jirgin saman Super Tucano don murkushe ‘yan ta’addan da suka tsere.