HomeLabaraiAn kai hari a taron PDP na Kaduna

An kai hari a taron PDP na Kaduna

Date:

Related stories

Gwamnatin Ribas ta soke amincewar amfani da filin wasanta wajen kamfen din Atiku

Gwamnatin jihar Ribas ta janye amincewarta na amfani da...

Babu wanda ya ke yakar Tinubu a fadar shugaban kasa, cewar gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba...

An kashe Fulani makiyaya 421 cikin watanni 3 a Najeriya – CPAN

Gamayyar kungiyoyin Fulani makiyaya ta Najeriya CPAN ta sanar...

‘Yan bindiga sun kai harin bam ofishin INEC

‘Yan  bindiga sun kaddamar da hari kan wani ofishin...

Majalisar dokokin Kano ta amince da daga darajar kwalejin Sa’adatu Rimi zuwa jami’a

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zartas da kudurin dokar...

Hankula sun tashi a filin wasa na Ranches Bees, harabar da jam’iyyar PDP ta gudanar da gangamin yakin neman zaben dan takararta na Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

Lamarin dai ya wakana ne yayin da wasu da ake kyautata zaton ’yan barandan siyasa ne sun kai hari kan magoya bayan jam’iyyar ta PDP a ranar Litinin din nan.

Aminiya ta ruwaito cewa, mahalarta taron dai sun rika neman mafaka yayin da ’yan barandan dauke da adduna sauran makamai iri-iri suka rika jifan mutane da duwatsu.

Haka kuma, an ruwaito cewa, ’yan daban sun yi wa jama’a da dama kwacen wayoyinsu na salula yayin taron.

Tuni dai tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Atiku ya yi martani kan wannan lamari da ya bayyana a matsayin abu takaici daga masu adawa da jam’iyyar PDP.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya gargadin magoya bayan sauran jam’iyyu da su shiga taitayinsu.

Atiku wanda ya tunatar da yadda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da tabbatar da aminci yayin yakin neman zabe, ya ce aukuwar wannan lamari a yanzu ya saba wa tsari na dimokuradiyya.

“Ina kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya ja hankalin dukkan magoya bayan jam’iyyu da su yi taka tsan tsan kan alkawarin tabbatar da zaman lafiya da suka dauka,” a cewar Atiku.

Mai Magana da Yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce tuni sun tura jami’ansu harabar domin kwantar da tarzoma.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories