Wani jirgin yaki ya fado a kasar Rasha

0
92

Wani jirgin saman soji ya fado kan wani gini da ke birnin Yeysk a kudancin Rasha bayan abin da ma’aikatar tsaron kasar ta ce ya samu matsalar inji ne.

Hotunan da ba a tabbatar da su ba a shafukan sada zumunta sun nuna wata babbar gobara da ta tashi daga wani bene mai hawa biyu a ranar Litinin

An gano jirgin da ya fadi a matsayin jirgin yakin Sukhoi Su-34. Sai dai ma’aikatan jirgin sun yi nasarar ficewa kafin jirgin ya fado, a cewar ma’aikatar tsaron Rasha.

Gobara ta lakume ginin, sakamakon man jirgin da ya zuba, kuma shaidun gani da ido sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Rasha Tass, cewa wutar tana ci ne daga hawa na farko zuwa hawa na tara. Yanzu haka dai jami’an kashe gobara na kokarin kashe wutar.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce “Yayin da yake kokarin tasghi sama daga filin jirgin saman soji na gundumar kudancin kasar, wani jirgin -34 ya yi hatsari.” “Musabbabin faduwar jirgin shi ne wutar da ta tashi a daya daga cikin injinan a lokacin tashinsa.”