Mbappe ya nesanta kansa daga batun sauya sheka

0
41

Kylian Mbappe ya yi watsi da rahotannin da ke yawo cewa yana shirn barin kungiyarsa ta Paris Saint-Germain a watan Janairu.

Mbappe wanda ya taka leda a wasan da PSG ta doke Marseille da ci 1-0 a ranar Lahadi, rahotanni na cewa dan wasan na zargin shugabannin kungiyar da yaudarar sa.

Dan wasan mai shekaru 23 da ya lashe gasar cin kofin duniya ya rattaba hannu kan wata sabuwar kwantiragi a watan Mayu, bayan watanni na rashin tabbas, amma an ruwaito cewa ya gaza samun kwanciyar hankali bayan kungiyar ta kasa biyan bukatunsa.

Mai baiwa PSG shawara Luis Campos ya musanta wadannan rahotannin inda ya ce Mbappe bai sanar da kungiyar irin wannan niyya ba, yayin da babban kocin kungiyar Galtier shima ya bayyana rudanin da suka shiga kan rade-radin.

A yanzu dai dan wasan na Faransa ya bayyana ra’ayinsa kan rahotannin da suka fito gabanin wasan da PSG ta buga da Benfica a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata, kuma ya ce ba gaskiya ba ne cewa yana shirin barin kungiyar nan ba da jimawa ba.

Real Madrid ta yi zawarcin Mbappe kafin ya amince ya tsawaita zamansa a Paris.