Wasu ‘yan bindiga sun kai hari coci a Kogi, sun kashe mutum biyu

0
81

An kashe mutane biyu, yayin da wasu uku suka jikkata yayin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai hari a wata Cocin Celestial da ke Felele, Lokoja, jihar Kogi.

DAILY POST ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a bayan tashar NNPC Mega da ke Felele.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan bindigar sun far wa cocin inda suka fara harbe-harbe ba da jimawa ba.

A cewarsa, ’yan daba sun mamaye Cocin inda suka fara harbi kan masu ibada.

“Abin takaici ne da jami’in ‘yan sanda na B Division Felele ya samu cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki wani cocin Celestial da ke bayan tashar NNPC, suka fara harbi.

“An tabbatar da mutuwar mutane biyu a asibitin, yayin da uku ke karbar kulawa.

“Kwamishanan ‘yan sanda ya tura jami’an mu, kuma ya umurci mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke gudanar da bincike, da ya fara bincike domin gano musabbabin harin da nufin kamo wadanda suka kai harin,” inji shi.

An kara samun labarin cewa mutane biyu ne suka mutu nan take, yayin da wasu da dama kuma suka yi tururuwa domin tsira da rayukansu.

Wadanda suka jikkata a halin yanzu suna karbar kulawa a cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FMC), Lokoja.

Wani ganau ya ce, “da suka shiga, sai suka fara harbin kowa a wajen cocin. Yanzu na je na buya a cikin gonar rogo. Abin da na gani jiya ya kasance kamar fim na wasan kwaikwayo a cikin fim. Kogi ba shi da lafiya”

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, (PPRO) William Ovye Aya ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar DAILY POST a safiyar ranar Litinin.