An kama mutum 80 da zargin taimakawa ‘yan bindiga a jihar Zamfara

0
105

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da kama wasu mutane 80 bisa laifin taimakawa ‘yan bindiga.

An mika wadanda ake zargin gidan yari ne bisa zarginsu da hannu dumu-dumu wajen aikata fashi da makami da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Abdullahi Shinkafi, Shugaban Kwamitin Hukunta ‘Yan Bindiga da Laifukan da ke da alaka da su, ya yi wa manema labarai jawabi a ranar Talata.

Wadanda ake zargin, wadanda suka hada da Mata, sun kasance masu bayar da bayanai ne, da kuma masu samar da abinci, da kwayoyi, da kakin soji da ‘yan sanda ga ‘yan bindigan.