Majalisar dokokin Nasarawa ta bukaci a sanya dokar ta baci kan harkar ilimi a matakin farko

0
50

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta bukaci kananan hukumomi da hadin gwiwar gwamnatin jihar da su dauki matakan da suka dace wajen daukar kwararrun .alamai a makarantun Firamare da ke fadin jihar.

Majalisar da cimma matsayar kiran gwamnatin jihar da ta gaggauta ayyana dokar ta baci ga fage ilimi a matakin farko.

Majalisar ta ce wannan kiran ya biyo bayan matsalolin da ake samu na rashin samar da ilimi mai inganci ne a matakin farko a fadin jihar.

Kazalika, sun ce, a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2021, akalla malama  Firamare 3,665 ne suka mutu ko suka kammala aikinsu ba tare an dauki sabbin ma’aikatan da za su maye gurabensu ba.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Ibrahim Balarabe Abdullahi, shi ne ya yi wannan kiran biyo bayan da Daniel Ogazi, shugaban kwamitin ilimi na majalisar ya bijiro da batun a kwaryar majalisar yayin zamanta na ranar Litinin a garin Lafia.

Kakakin ya kara da cewa, muddin aka dauki malaman da suka dace don su jagoranci harkokin ilimi a makarantun Firamare hakan zai taimaka sosai wajen farfado da harkokin ilimi a fadin jihar.