Dan takarar Shugaban Kasa na Jamâiyyar APC, Sanata Bola Tinubu, ya sha alwashin hako mai a Arewa da kuma inganta tsaro muddin aka zabe shi magajin Shugaba Buhari a 2023.
Tinubu ya ce zai hako arzikin mai da Najeriya ke da shi a Binuwai da yankin Tabkin Chadi, kana ya bai wa fannin tsaro muhimmanci don amfanin alâummar kasa.
Dan takarar ya yi wannan alwashi ne yayin da yake jawabi a wajen taron da wasu kungiyoyin Arewa suka shirya ranar Litinin a Kaduna.
Kungiyoyin sun shirya taron ne domin jin irin burin da dan takarar ke da shi na bunkasa Arewa idan Allah Ya ba shi mulkin kasa.
A cewar Tinubu, akwai tarin arzikin fetur da iskar gas a Binuwai da yankin Tabkin Chadi da sauran wurare a Arewacin kasar nan.
âAikin samar da gas din zai taimaka ainun wajen kafa masanaâantu a yankunan da kuma tara kudin shiga don amfanin kasa,â in ji shi.
Kazalika, dan takarar ya yi alkawarin karasa aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano da kuma aikin shimfida bututun gas da ake kan gudanarwa.
Tshohon Gwamnan na Jihar Legas, ya yi waiwaye kan irin nasarorin da ya samu a lokacin da ya rike Jihar Legas, yana mai cewa, zai ninka korkarin da ya yi a wancan lokaci wajen bunkasa kasa baki daya.