HomeLabaraiTinubu ya yi alkawarin hako mai da inganta tsaro a Arewa

Tinubu ya yi alkawarin hako mai da inganta tsaro a Arewa

Date:

Related stories

Hukumar DSS ta kama wasu bata gari da ke sayar da sabbin takardun kudi na Naira

Ma’aikatar harkokin wajen kasar a ranar Litinin din nan...

Yadda lamari ya kasance yayin zuwan Buhari Kano don kaddamar da aiyuka 8

An tsauraran matakan tsaro a cikin birnin Kano da...

Najeriya ta yi asarar likitoci 2800 a cikin shekaru biyu – NARD

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya NARD, Dr Innocent Orji ya...

Yadda ake canzar da kudin Sepa zuwa Naira a yau Litinin

Farashin Separ Nijar zuwa Naira a farashin kasuwar canjin...

Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Sanata Bola Tinubu, ya sha alwashin hako mai a Arewa da kuma inganta tsaro muddin aka zabe shi magajin Shugaba Buhari a 2023.

Tinubu ya ce zai hako arzikin mai da Najeriya ke da shi a Binuwai da yankin Tabkin Chadi, kana ya bai wa fannin tsaro muhimmanci don amfanin al’ummar kasa.

Dan takarar ya yi wannan alwashi ne yayin da yake jawabi a wajen taron da wasu kungiyoyin Arewa suka shirya ranar Litinin a Kaduna.

Kungiyoyin sun shirya taron ne domin jin irin burin da dan takarar ke da shi na bunkasa Arewa idan Allah Ya ba shi mulkin kasa.

A cewar Tinubu, akwai tarin arzikin fetur da iskar gas a Binuwai da yankin Tabkin Chadi da sauran wurare a Arewacin kasar nan.

“Aikin samar da gas din zai taimaka ainun wajen kafa masana’antu a yankunan da kuma tara kudin shiga don amfanin kasa,” in ji shi.

Kazalika, dan takarar ya yi alkawarin karasa aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano da kuma aikin shimfida bututun gas da ake kan gudanarwa.

Tshohon Gwamnan na Jihar Legas, ya yi waiwaye kan irin nasarorin da ya samu a lokacin da ya rike Jihar Legas, yana mai cewa, zai ninka korkarin da ya yi a wancan lokaci wajen bunkasa kasa baki daya.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories