’Yan Bindiga sun kashe mutum 3 a Filato

0
65

’Yan bindiga da ba san ko su wane ne ba sun kashe Mai Unguwar kayuen Nyalum, Salisu Idris, da wasu mutum biyu a Karamar Hukumar Wase ta Jihar Filato.

’Yan bindigar da suka isa kauyen a kan babura sun kuma yi garkuwa da wasu biyar tare da sace babura da dama a harin  da suka kai kauyen ranar Litinin da dare.

Shugaban Kungiyar Matasan Wase, Shafi’i Sambo, ya shaida wa Aminiya cewa, “Maharan sun so daya a kan babura suna harbi kan mai uwa da wai, suka wuce kai tsaye suza gidan basaraken, suka kashe shi, sannan suka tafi da mutum biyar daga gidan.

“Sun kuma kashe wasu mutum biyu kafin su shiga gidan,” in ji Shafi’i, wanda ya ce, maharan sun kuma sace babura da dama a kauyen.”

Wani mazaunin kauyen ya ce daga cikin mutanen biyar da ’yan bindigar suka yi awon gaba da su har da matan basaraken biyu.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Filato, DSP Alabo Alfred, ya ce mutum uku sun rasu bayan maharan sun yi harbi kan mai uwa da wabi a cikin dare, sai dai har yanzu babu cikakken bayani game da harin.