Bamu cimma matsaya ba akan siyan Erling Haaland – Perez

0
114

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Florentino Perez ya ce ba shi da masaniyar komai game da batun yarjejeniyar sakin Erling Haaland daga Manchester City.

Haaland ya koma Etihad ne a wannan kakar daga Borussia Dortmund, inda a cikin wasanni 14 da ya bugawa City, ya zura kwallaye 20.

Real Madrid na daga cikin kungiyoyin da suka nuna sha’awar sayo dan wasan a lokacin bazara kuma har yanzu ana ci gaba da alakanta Los Blancos din da zawarcinsa.

Ana kuma hasashen cewa, Real Madrid ce zata kasance kungiyar da Haaland zai koma in ya bar City, sai dai kalaman shugaban Madrid Perez na nuna cewar zakarun na La liga basu shiryawa hakan ba.

A kalaman na Perez ya ce a yanzu suna kwararrun ‘yan wasa don haka basa bukatar wani.

Idan dai ba’a manta ba, a lokacin wata ganawa da aka yi da Perez a birnin Paris a farkon wannan makon ya ce Real Madrid ba ta da wata aniyar sake zawarcin dan wasan gaban PSG Kyalia Mbabape.