Wata gobara ta kama wani gidan man sayar da gas da ke gefen gadar Obirikwere ta hanyar Gabas ta Yamma a garin Fatakwal a Jihar Ribas.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Laraba.
Wani jami’in hukumar kashe gobarar ya ce gobarar ta tashi ne sakamakon “hujewar tankin motar gas” a gidan man.
Kawo yanzu ba a bayyana adadin wadanda suka mutu ba amma shaidun gani da ido sun ce akalla mutane uku ne gobarar ta shafa.