Gobara ta tashi a wani gidan man sayar da Gas a Fatakwal

0
54

Wata gobara ta kama wani gidan man sayar da gas da ke gefen gadar Obirikwere ta hanyar Gabas ta Yamma a garin Fatakwal a Jihar Ribas.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Laraba.

Wani jami’in hukumar kashe gobarar ya ce gobarar ta tashi ne sakamakon “hujewar tankin motar gas” a gidan man.

Kawo yanzu ba a bayyana adadin wadanda suka mutu ba amma shaidun gani da ido sun ce akalla mutane uku ne gobarar ta shafa.