Kante ba zai buga gasar cin kofin duniya ba

0
98

Dan wasan tsakiya na Faransa da Chelsea N’Golo Kante ba zai buga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar ba sakamakon zaman jinya da dan wasan zai yi.

Kante, mai shekaru 31, ya samu raunin ne a wasan da Chelsea ta buga 2-2 a gida da Tottenham ranar 14 ga watan Agusta.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce an samu nasarar aikin da aka yiwa dan wasan a kafarsa, amma ana sa ran Kante zai yi jinyar watanni hudu.

Sanarwar ta ce “Dan wasan tsakiyar ya ziyarci sashen kula da lafiya na kulob din don gano hanyoyin da ya kamata ya bi wajen samun buga babbar gasar ta duniya.

Kocin Chelsea, Graham Potter ya ce kafin kungiyarsa ta buga wasa da Aston Villa a karshen makon da ya gabata, Kante ya fuskanci koma baya a yunkurinsa na dawo da karsashinsa.

Kante, wanda ya lashe gasar cin kofin duniya da Faransa a shekarar 2018, ya shiga jerin ‘yan wasan Premier da suka samu munanan raunuka.

Abokin wasansa na Chelsea Reece James na cikin shakku sosai a Ingila bayan raunin da ya ji a gwiwarsa a karawar da suka yi da AC Milan a gasar cin kofin zakarun Turai a watan nan.

A ranar Talata, fatan dan wasan gaban Liverpool Diogo Jota na wakiltar kasar Portugal ya gamu da cikas, bayan da Jurgen Klopp ya tabbatar da cewa dan wasan mai shekaru 25 zai yi jinya na tsawon lokaci saboda raunin da ya samu.