Ministan harkokin wajen Mali ya zargi Faransa da yin leken asiri

0
63

Ministan harkokin wajen Mali ya ce gwamnatin sojan kasar za ta yi amfani da ‘yancinta na kare kanta idan Faransa ta ci gaba da zagon kasa ga ‘yancin kai da tsaron kasar.

Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Mali a birnin New York, minista Abdoulaye Diop ya sake nanata zargin cewa Faransa ta keta sararin samaniyarta tare da kai makamai ga mayakan Islama da ke kai hare-hare a arewacin Mali shekaru goma da suka gabata.

Faransa ta musanta hakan.

Dangantakar ta da kasar Mali ta yi tsami ne tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Agustan shekarar 2020, kuma tana janye sojojin da aka aika a shekarar 2013 domin taimakawa wajen yakar ‘yan tawaye.

“Akwai bukatar gudanar da wani taro na musamman na komitin sulhu wanda zai ba mu damar fito da wasu hujjoji dangane da wasu abubuwa na ban mamaki, ayyukan leken asiri da kuma tada zaune tsaye da Faransa ke yi,” in ji Diop.

Ya kara da cewa “Gwamnatin Mali na da hakkin yin amfani da ‘yancinta na kare kanta…idan Faransa ta ci gaba da zagon kasa ga ‘yancin kan kasarmu da kuma lalata yankinta da tsaronta.”

Wakilin Faransa a Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da wannan zargi da cewa cin mutunci ne, ya kuma kare tsoma bakin Faransa a Mali a matsayin gaskiya, sannan ya ce kasar ba ta taba keta sararin samaniyar Mali ba.