Gwamnatin Kogi ta maka Dangote a kotu kan takaddamar kamfanin simintin Obajana

0
81

Gwamnatin Jihar Kogi ta shigar da karar kamfanin Dangote kan batun wanda ke da mallakar kamfanin siminti da ke Obajana a jihar.

Babban mai taimaka wa gwamnan kan yada labarai, Mohammed Onogu, ya tabbatar wa manema labarai, inda ya ce sun shigar da karar ne a ranar Laraba a gaban babbar kotun jihar da ke Lokoja.

Ya ce gwamnatin na fatan kotu za ta yi duba na tsanake kan yarjejeniyar da ke tsakanin kamfanin Dangote da Jihar
Kogi da aka cimma ranar 30 ga watan Yulin 2002 da kuma ran 14 ga Fabrairun 2003.

Sai dai har yanzu kamfanin Dangoten bai ce uffan ba kan batun.

Wannan kara da gwamnatin Kogi ta shigar na nuna cewa sulhu da shiga tsakanin da gwamnatin tarayya ta yi a makon da ya gabata bai yi tasiri ba.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Jihar Kogi ta rufe kamfanin simintin bisa zargin cewa bai bi ka’ida ba wajen mallakar hannun jarinsa ba.

Sai dai a martanin da kamfanin Dangote ya yi tun a lokacin, ya ce ya zuba jari a kamfanin simintin na Obajana, kuma ya bi dukkan ka’idojin da suka dace kafin ya fara harkar siminti a jihar.

A cikin karar da gwamnatin jihar ta shigar, ta nemi kotun da ta soke yarjejeniyar bisa hujjar cewa ba ta cika sharudanta ba, wadanda su ne ginshikin ingantaccen kwantiragi.

Gwamnatin jihar na kuma son kotu ta hana kamfanin Dangote cin gajiyar riba ko samun wata dama daga yarjejeniyar ta 2002 da 2003, saboda rashin bai wa gwamnatin jihar wasu muhimman bayanai kan matsayarta a kan yarjejeniyar.

Kazalika tana so a soke dukkan yarjejeniyar da aka kulla tsakaninta da kamfanin Dangote.

Tun da farko Dangote ya yi kunnen uwar shegu da bukatar kirayen da suka yi masa kan amsa wasu tambayoyi da ta shirya masa.

Daga bisani kuma Gwamnatin Tarayya ta shiga tsakani don ganin an yi sulhu, amma abun ya ci tura.