‘Yan sandan Benue sun kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne

0
62

Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe ta kama wasu mutane tara da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da ke addabar al’ummar Adoka da kewaye a karamar hukumar Otukpo ta jihar.

Wadanda ake zargin, ciki har da wata budurwa, ana zarginsu da kona gidaje.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Wale Abass, ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun kusa mamaye al’ummar Adoka da kewaye.

“Lokacin da wadannan mutane suka yi barna, sai su tsere cikin daji. Na baya-bayan nan dai shi ne kona gidaje biyar a Adoka a ranar Asabar din da ta gabata.

Abass ya ce: “Abin farin ciki, mutanenmu sun samu nasarar cafke wasu daga cikinsu kuma an kawo su hedikwatar da ke Makurdi.”

Wani shugaban al’ummar da ya bayyana kansa da Obaje Gabriel ya shaida wa manema labarai cewa wadanda ake zargin sun kawo cikas ga zaman lafiyar al’ummar Adoka tsakanin Asabar da Lahadi.

“Wadannan yaran sun dage cewa dole ne su mamaye kauyen; suna shan kwayoyi suna yin duk abin da suka ga dama. Wani lokaci, za su rika zagin dattawa a kan titi suna cewa babu wanda zai iya yi musu komai.

“Sun kona gidaje biyar a ranar Asabar da Lahadin da ta gabata,” in ji Gabriel.

Mace daya tilo a cikin wadanda ake zargin da taki a bayyana sunanta ta ce tana kokarin shiga tsakani ne kawai a fada lokacin da aka kama ta.