Dalilinmu na titsiye ’yan takarar shugaban kasa – Dattawan Arewa

0
61

A farkon makon nan ne wasu kungiyoyin Arewa a karkashin jagorancin Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) da Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) suka jagoranci wasu kungiyoyi wajen shirya taron ganawa da ’yan takarar Shugaban Kasa domin titsiye su su bayyana shirye-shiryensu musamman ga Arewa idan sun samu nasara.

An shirya taron ne a karkashin kungiyoyin Arewa shida da suka hada da Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) da Kungiyar ACF da Gidauniyar Tunawa da Sardauna da Jam’iyyar Matan Arewa da Shirin Bincike da Bunkasa Ci-gaban Arewa (ARDP).

Sai dai lamarin ya tayar da kura, musamman bayan wata wasika ta fito daga dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, inda a ciki ya ce ba zai halarci taron ba, sannan a karshen wasikar ya bayyana cewa yana ba kungiyoyin shawara su guji sanar da mutum daya a matsayin dan takarar Arewa.

Dalilin shirya taron – Hakeem Baba-Ahmed

Aminiya ta zanta da Dokta Hakeem Baba-Ahmed, wanda shi ne Kakakin Kungiyar Dattawan Arewa, inda ya bayyana makasudin shirya taron.

Game da dalilin shirya taron, Dokta Hakeem ya ce, “Mun lura ba a taba irin wannan ba.

“A tara ’yan takara masu neman shugaban kasa ko gwamnoni su fada wa duniya abin da za su yi idan Allah Ya ba su shugabanci musamman a Arewa.

“Kuma muka ga za mu iya yi, domin muna da kima da daraja a idanunsu sannan kuma jama’a za su amfana.

“Shi ne muka gwada, kuma alhamdulillahi, Allah Ya albarkaci abin.

“Mun kira mutum shida daga ranar Asabar zuwa ranar Litinin kuma biyar sun zo.

“Dan takara ya san cewa an sa masa ido, mun tsugunar da kai mun ce fada wa jama’a abubuwan da za ka yi a fannin tsaro da ilimi da gyara Arewa ta dawo mana da kimarmu a Najeriya.

“Yanzu nan dattawa ne da kungiyoyin Arewa da kuma jama’a ga kuma talabijin ga rediyo suna ji.

“Sannan idan ka fita kana kamfe za mu bi ka da wadannan alkawura.

‘Za mu bayyana dan takararmu idan ta kama’

“A karshe muna so mu tantance mu gani idan ya zama dole mu ce mu muna gani za mu bi wanda muke ganin zai fi yi wa Arewa da Najeriya amfani.

“In ya zama dole mu ce za mu ce wane ne, in kuma bai zama dole ba akalla dai mun fito wa jama’a yadda za su gane ’yan siyasar burun-burun da kuma na kirki.

Kwankwaso ba shi da abin fada – Baba-Ahmed

“Game da zargin da ake yi cewa an shirya taron ne domin tsayar da dan takara daya daga Arewa, Dokta Hakeem ya ce, “A’a, wannan dan takara da ya ce ba zai zo ba maganarsa ce kawai ya yi, ba ya dai da abin da zai yi ne idan ya zo wajen, ya sa ya fito ya yi wannan kazafi.

“Na daya dai ba ya da shaida, kuma ai ba cewa ya yi saboda za a fitar da dan takara ba ne, cewa ya yi wai an saye mu.

“Da ya fara da cewa yana da wasu ayyuka lokaci ne bai yi masa daidai ba, daga baya sai ya kare da cewa ai abin ma gaba daya wani dan takara ya saye mu.

“Mun yafe masa duniya da Lahira sai dai kuma idan siyasar yake yi a yanzu, yana cikin matsala saboda a ce dan siyasa kuma na Arewa ana wannan abu a Kaduna an ce zo ka tsaya ka gaya wa jama’a, biyar sun zo shi bai zo ba abin dubawa ne.

“A yanzu haka wadanda ba mu kira ba suna nan suna tambaya su yaushe za a kira su. Sai kai kadai?

“In dai yana da matsalarsa ya je can.

“Mu dai abin da muka yi niyyar yi shi ne mu tara ’yan takara shida da muke ganin kila a samu daya daga cikinsu Allah Ya ba shi nasara.

“Ya ce shi ba zai tsaya a gaban jama’a ya fada musu abin da zai yi ba, to shi da jama’a.

Yadda za mu fitar da dan takara – Dattawan Arewa

“Idan kuma za mu fito da dan takara daga ciki wannan shawarar za mu duba ko za mu ce wani ne muke gani ya fi cancanta ga ’yan Arewa su jefa masa kuri’a ba a yanzu za mu yi wannan abu ba.

“Sai mun sa ido mun gani za mu bi su kamfe mu ga wasu abubuwa da za su yi.

Zargin an saye dattawan Arewa

Kan batun an ba su kudi kuwa cewa ya yi, “’Yan siyasa gani suke yi kowa kamarsu ne.

“Akwai mutane wadanda alhamdulillahi kudi dai wannan da ake kashewa wallahi ba zai iya sayenmu ba.

“Komai kudinka ba za ka iya sayen mu ba, ballantana ka ce a shirya maka wani abu.”

Ya kamata a dauki darasi

A karshe Dokta Hakeem ya yi kira ga masu zabe su hankalta su yi amfani da abubuwan da suka koya a taron da suka shirya.

“Ka ga yanzu idan akwai wani a cikinsu da ya yi mana alkawura za mu bi su mu ce ka tuna lokacin da ka zo Gidan Arewa ka ce za ka yi kaza da kaza, ba mu gani ba ko kuma mun gani.