HomeLabaraiGwamnati ta daukaka kara kan sallamar Kanu da kotu ta yi

Gwamnati ta daukaka kara kan sallamar Kanu da kotu ta yi

Date:

Related stories

Hisbah ta amince da sahihancin auren matar da ta auri saurayin ‘yarta a Kano

Hukamar Hisbah ta jihar Kano ta gamsu da sahihancin...

Kashi 50 na magungunan Afrika jabu ne

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar sama da...

Manchester United ta yi aron Sabitzer daga Munich don cike gurbin Eriksen

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta karbi aron...

Chelsea ce mafi kashe kudi a kasuwar musayar ‘yan wasan Firimiya ta bana

A daren jiya talata ne aka kammala kulle kasuwar...

Sarkin Dutse Nuhu Sunusi ya rasu

Allah ya yi wa Sarkin Dutse Alhaji Dr. Nuhu...

Gwamnati ta daukaka karar ne tana zargin Kanu da ta’addanci da cin amanar kasa.

A makon jiya ne alkalan kotun guda uku, karkashin jagorancin Mai Shari’a Jummai Hanatu Sankey suka yi watsi da sauran laifuffuka bakwai da gwmanati ta zargi Kanu da aikatawa, bisa hujjar take dokar kasa da kasa yayin kamo shi daga Kenya.

Sai dai Babban Lauyan Kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce sallamar Kanu kawai kotun ta yi amma ba ta wanke shi daga laifuffukan da ake zargin sa da su ba kafin tserewarsa a Satumba, 2017.

A cikin karar da ta shigar Kotun Koli ranar Talata, gwamnati ta ce Kotun Daukaka Kara ta yi kuskure wajen soke sauran laifuffukan da ake zargin Kanu da su, inda ta ce Babbar Kotun Tarayyar da aka shigar da karar da farko ba ta da hurumin sauraren karar.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories