Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba da sanarwar sayar da Bankin Polaris tare da bayyana sabon mamallakin bankin.
Daraktan Sadarwa na CBN, Osita Nwanisobi, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, yanzu Bankin Polaris ya koma hannun kamfanin zuba jari na Strategic Capital Investment Limited (SCIL).
Nwanisobi ya ce, an cimma matsayar sayar da bankin ga SCIL ne tsakanin CBN da kuma Kamfanin Kula da Kadarorin Gwamnati (AMCON).
Bankin ya rikide ya koma Polaris ne a 2018 bayan da CBN ya shiga tsakani ya kwace lasisin tsohon Bankin Skye.
Daga nan CBN ya bai wa bankin rance na makudan kudi biliyan N898 ta hannun AMCON, wanda ya kamata ya biya a cikin shekara 25.
Sanarwar ta ce CBN ya dauki wadannan matakan ne domin hana bankin rugujewa, kare kudaden ajiyar mutane, kare ayyuka da sauransu.
Kazalika, sanarwar ta ce SCIL ya biya kafin alkalami na biliyan N50 tare da amincewa da dukkan sharuddan da aka gindaya masa.