Ba ni da niyyar barin PSG – Mbappe

0
115

Dan wasa Kylian Mbappe ya ce bai taba cewar zai bar kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain a watan Janairu ba kuma bashi da niyyar tafiya, bayan rahotan da ke cewar dan wasan zai bar kungiyar a bana.

A cikin watan Mayu dan kwallon tawagar Faransa mai shekara 23 a duniya ya saka hannu kan yarjejeniya mai tsoka, domin ci gaba da buga wasa a PSG duk da cewa tun a baya can an yi ta alakanta Mbappe, wanda ya lashe kofin duniya da Fransa a Rasha a shekarar 2018 da cewar zai koma Real Madrid buga wasa.”Ina cikin farin ciki a PSG ban taba cewar zan bar PSG a watan Janairu ba.”

kamar yadda Mbappe ya bayyana, bayan tashi wasan Paris St Germain da ta ci Marseille 1-0 ranar Lahadi a karawar mako na 11 a Ligue 1.

Kuma shi ne ya bai wa Neymar kwallon da ya ci, kuma ta 200 da dan wasan tawagar Brazil ya zura a raga tun daga Santos da Barcelona da PSG.

Wani rahoto ya bayyana a lokacin da PSG za ta kara da Benfica a Champions League ranar Talata, inda aka ce Neymar baya jin dadin zama a PSG kuma rahoton ya kara da cewar kungiyar ta Faransa ta yi masa romon baka – zai bar PSG a watan Janairu, idan an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo.