HomeLabarai'Yan arewa sun kira ni limamin coci saboda Jonathan - Lamido

‘Yan arewa sun kira ni limamin coci saboda Jonathan – Lamido

Date:

Related stories

Manyan kabilar Fulani suna so su ga bayana – Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya koka da cewa...

Kotu ta raba auren ‘yar Ganduje da shafe shekaru 16

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano...

Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

Wata kotu a Kano ta aika da Murja Ibrahim...

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce, ya sha zazzafar caccaka, inda har wasu suka kira shi da suna fasto, wato limanin coci a arewacin Najeriya sakamakon goyon bayan da ya nuna wa tsohon shugaba kasar,fa Goodluck Jonathan.

Lamido ya fadi haka ne a wata hirarsa da tashar talabijin ta Arise, batun da yanzu ke ci gaba da yamutsa hazo a shafukan sada zumunta, yana mai cewa, Jonathan ya zama abin da ya zama a yanzu ne saboda yin watsi da lamurran jam’iyyarsu ta PDP.

Lamido ya ce, yana takaicin yadda Jonathan ya zama a yanzu, wanda shekaru 10 da suka shude babu wanda ya san sa a Najeriya, amma ya yi fice albarkacin jam’iyyar PDP wadda ta yi masa komai a rayuwarsa a cewarsa.

Lamido ya ci gaba da fadin cewa, an kira shi da suna fasto, sannan ana ta yi masa kallon watsattse a yankin arewacin Najeriya  saboda yadda ya yi tsayin-dka kan Jonathan.

An kira ni da suna fasto a arewa saboda Jonathan. Na tsaya masa duk wuya duk runtsi. A arewa, an yi min kallon wani watsattse wanda ke yaki da manufofin arewa saboda amannar da na yi wa Najeriya. inji Lamido.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories