Sarki Charles zai sanya dawakan sarauniya Elizabeth guda 14 a kasuwa zai sayar

0
85

BBC ta rawaito cewa, Sarki Charles na uku zai sayar da wasu daga cikin dawakan da ya gada daga mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.

Marigayiya Sarauniya ta kasance mai son dawaki kuma tana kiwonsu.

Gidan gwanjon kayayyaki na Tattersalls ya ce zai yi gwanjon dawaki 14 na Sarauniya a yau Litinin.

Daga cikin dawakin har da Just Fine wanda ya lashe tsere kusan 100.

Kakakin gidan gwanjon na Tattersalls ya ce ba wani sabon abu bane saboda a duk shekara suna sayar da dawaki.