Buhari ya bai wa Ministan ruwa wa’adin wata 3 don kawo karshen ambaliyar ruwa a Najeriya

0
77

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Albarkatun Ruwa da yayi jagoranci tare da hada kai da ma’aikatun Muhalli da Sufuri da kuma gwamnatocin jihohin kasar domin samar da wani cikakken tsari na dakile iftila’in ambaliyar ruwa a fadin Nijeriya.

Umarnin na Buhari, wanda aka mika wa ministan cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya ce an gabatar masa da shirin nan da kwanaki 90.

Wata sanarwa da Garba Shehu ya fitar a ranar Litinin, ta bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.

Ya kuma kara da cewa, shugaba Buhari yana karbar bayanai akai-akai kan halin da ake ciki na ambaliyar ruwa a kasar tare da jaddada aniyarsa na magance kalubalen da iftila’in ya haifar a kasar.

Babu tabbas ko umarnin shugaban kasar na cikin martani ne ga sukar da wasu ‘yan Nijeriya ke yi na zargin gwamnatin tarayya da yin shiru kan kalubalen ambaliyar ruwa.