ECOWAS ta ce ya zama wajibi Najeriya ta gudanar da sahihin zabe

0
49

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta roki hukumomin Najeriya da su tashi tsaye, wajen ganin kasar ta gudanar da sahihin zabe a shekara mai zuwa saboda muhimmancin ta ga Afirka baki daya.

Tawagar kungiyar da ta ziyarci Najeriya domin ganin shirin zaben a karkashin tsohon shugabar hukumar zaben Ghana, Dr Kwadwo Afari-Gyan, ta bayyana haka ne lokacin da ta gana da shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmud Yakubu a birnin Abuja.

Daraktan yace kungiyar ECOWAS ta bayyana fatar ganin zaben na shekara mai zuwa ya gudana ba tare da matsala ba, saboda irin jagorancin da Najeriya ke bayarwa a yankin.

Shugaban bangaren siyasa na kungiyar ECOWAS, Dr Remi Ajibewa yace sun ziyarci Najeriya ne domin ganin yadda shirin zaben ke gudana kamar yadda dokar kungiyar ta tanada.

Ajibewa yace kudirorin kungiyar sashe na 11 da 12 da 13 sun baiwa kungiyar damar tura jami’an sa ido kowacce kasa dake yankin duk lokacin da za’a gudanar da zaben shugaban kasa.

Saboda haka jami’in yace ziyarar da suka kai Najeriya ba itace ta farko ba, domin duk lokacin da za’a gudanar da zabe sukan yi haka.