Kotu ta bada umarnin kwace wasu kadarorin Diezani Alison Madueke a Abuja

0
87

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta bayar da umarnin kwace gidaje biyu, tare da motocin alfarma guda biyu na tsohuwar ministar man fetur da albakatun kasa, Diezani Alison-Madueke.

A wata sanarwa da EFCC, ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce gidan tsohuwar ministar mai lamba 1854 a kan titin Mohammed Mahashir, da kuma dayan mai lamba 6 Aso Drive, na a unguwannin Maitama da Asokoro da ke Abuja babban birnin kasar.

Hukumar ta ce darajar gida dayan ta kai Dala 2,674,418, dayan kuma darajarsa ta kai Naira miliyan 380,000,000.

Mai shari’a Mobolaji Olajuwan na Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ne, ya zartar da hukuncin karbe wasu kadarori; ciki har da wasu motoci biyu na alfarma a ranar Litinin.

EFCC ta ce kadarorin mallakin tsohuwar ministar mai da albakatun kasa ne, Misis Diezani Alison Madueke