‘Yan bindiga sun sace mutane da dama a harin awa 4 a Kaduna

0
78

An shiga tashin hankali bayan ’yan bindiga sun kai hari da tsakar rana suka shafe awa hudu suna harbe-harbe tare da yin awon gaba da mutane a Jihar Kaduna.

Wani mazaunin kauyen Autan Kuli da ke gundumar Yakawada, Karamar Hukumar Giwa ta jihar, ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun yi awon gaba da mutum shida da yammacin ranar Alhamis.

Ya ce maharan da ake zargin ’yan fashin daji ne sun kai farmakin ne da misalin karfe 2 na rana zuwa karfe 6 na Magriba, suka tisa keyar mutum shida suka tafi da su.

Kawo yanzu mutum 60 ke nan ’yan bindiga suka sace yankin Karamar Hukumar Giwa cikin kasa da kwana 10.

A cikin makon nan ne Aminiya ta kawo rahoton yadda ’yan bindiga suka sace mutum 54 a karamar hukumar, cikin mako biyu.

Mazauna yankunan sun ce tun da aka shiga watan Oktoba da muke ciki, kusan kullum sai ’yan bindiga sun sace musu ’yan uwa.

Da yake bayani kan harin ranar Alhamis, wani dan sa-kai a kauyen Autan Kuli ya ce wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da Usman Mai Unguwa, Mashakuru Audu, Umma Nasiru, Hauwa Nasiru, Jamilu umar, da kuma Sunusi Bashari.

Ko a daren ranar Talata, ’yan  bindiga sun shiga kauyen Hayin Malam da ke gundumar Jama’a da ke makwabciyarsu, Karamar Hukumar Sabon Garim inda suka dauke mutane biyu.

Majiyar kungiyar ’yan sintiri ta yankin ta shaida wa wakilinmu cewa, “Da misalin karfe 11.30 na dare maharan suka afka wani gida da ke layin Shaka a Hayin Malam inda suka yi gaba da wani mai suna Musa Omeza da kuma Fatima Hassan, bayan sun yi ta harbe harbe.”

Sai dai ya ce bayan afkuwar al’amarin, ’yan kungiyar sintiri ta yankin sun yi kokarin bin maharan don kwato mutanen, amma hakan bai yiwu ba, saboda sun kasa gano hanyar da suka bi.

Wakilinsmu ya kira Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, har sau uku, domin samun karin bayani, amma babu amsa.