Akwai yuwuwar a haramtawa Tunisia halartar gasar cin kofin duniya – FIFA

0
75

Za a iya haramtawa Tunisiya halartar gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a wata mai zuwa idan gwamnatin kasar ta tsoma baki a harkokin kwallon kafa, in ji hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa.

FIFA ta ce dole ne mambobinta su nesanta kan su daga tsoma bakin kan lamuran da suka shafi siyasa.

Gargadin na zuwa ne bayan kalaman da ministan matasa da wasanni na Tunisia, Kamel Deguiche ya yi, game da yuwuwar rushe ofisoshin gwamnatin tarayya.

Fifa dai na kallon furucin nasa a matsayin wani yunkuri na yin katsalandan a harkokin gudanarwar hukumar kwallon kafa ta kasar, kuma ta bukaci hukumar da ta yi karin haske game da yunkurin tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida da kuma barazanar rusa ofishinta.

Hukumar mai shalkwata a Zurich ta kuma tunatar da cewa kungiyoyin mambobi ya wajaba a kan su gudanar da al’amuransu ba tare da wata mu’amala ta siyasa ba.