CBN da Ministar Kudi sun sa zare kan batun sauya takardun kudi

0
94

Dambarwar sauyin takardun kudade ta dauki sabon salo, inda Babban Bankin Najeriya (CBN) da Ma’aikatar Kudi da Kasafi da Tsare-tsare ke nuna wa juna yana.

Wannan na zuwa ne bayan Ministar ma’aiakatar, Zainab Ahmed, ta nesanta ma’aikatarta da shirin, kwana biyu bayan bankin CBN ya sanar da shi.

Ministar ta nesanta ma’aitarta da matakin ne CBN ne bayan kwamitin ya bayyana damuwa cewa a kasa da kwana biyu da sanar da shirin, farashin Dala ya tashi daga N740 zuwa N788.

A amsarta, sai ta ce, “CBN bai tuntube mu a Ma’aikatar Kudi ba kafin yanke shawarar sauya wasu takardun Naira ba, don haka su ne za su iya amsa wannan tambayar.

“Amma a matsayina na babbar jami’a a haskar tsare-tsaren kudi a Najeriya, wannan tsarin da ake shirin aiwatarwa na da matukar hadari ga darajar Naira.”

Sa’o’i kadan bayan nan ne aka ji Babban Bankin ya fito ya yi bayani da ake gani martani ne a gare ta.

A ranar Juma’a ne ministar, ta bayyana wa Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawa cewa CBN bai nemi shawarar ma’aikatarta ba kan sauyin takardun kudaden da ya ce zai fara aiki daga ranar 15 ga watan Disamba.

Ta kuma bayyana cewa matakin na CBN a irin wannan lokaci, zai iya kara karya darajar Naira a kasuwar canjin kudade.

Sa’o’i kadan bayan bayanin Ministar, Kakakin CBN, Osita Nwanisobi, ya bayyana mamakin kalamanta, yana mai cewa babu abin da CBN ke yi ba tare da ta bi.

A cewarsa, CBN ya cika duk kai’odijin da suka dace ba, kuma ya bi duk ka’idoji da suka kamata kan sauya takardun Naira 200 da 500 da kuma 1,000, wanda hasali tun shekara 12 da suka gabata ya kamata a yi.

Ya bayyana cewa a ka’ida, bayan duk shekara biyar zuwa takwas ya kamata CBN ya buga, ya kuma fitar da sabbin kudade, amma wannan karon sai da ya yi jinkirin shekara biyar.

Nwanisobi ya kara da cewa, kamar yadda Dokar CBN ta 2007 ta tanadar, sai da Hukumar Gudanarwar bankin ya rubuta a hukumance ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tana neman amincewarsa, kuma ya sahale mata sabunta fasali, bugawa da kuma fitar da sabbin takardun N200 da N500 da kuma N1,000.

Ya roki al’ummar Najeriya da su goyi bayan matakin, wanda ya ce an yi da kyakkyawan nufi domin amfanin kasa baki daya.

Ya bayyana cewa babu wata boyayyiyar manufa a sauyin kudaden, kuma bankin ya yi haka ne domin karfafa tsarin rage amfani da kudi na zahiri da kuma rungumar kudin intane na e-Naira.

A cewarsa akwai dimbin mutake da ke suka makare gidajensu da takardun kudade, wanda ya ce bai kamata a bari hakan ya ci gaba da faruwa ba.

Idan ba manta ba, tun a lokacin da bakin ya sanar da fara amfani da sabbin takardun kudaden daga ranar 15 ga watan Disamba, da kuma soke amfani da tsoffin daga ranar 31 ga watan Janairun 2023 ta bayyana dalilan yin haka.

Dalilan sun hada da magance hauhawar farashi, karya tattalin ’yan ta’adda da ke rike da makuden kudade a cikin daji, toshe kofar safarar haramtattun kudade, kare Naira daga masu yin jabun kudade, kawar da takardun kudade da suka dagargaje da sauransu.