Babu wanda ya isa ya sauke ni daga shugabancin PDP – Ayu

0
92

Shugaban babbar jam’iyyar hamayya ta PDP Dakta Iyorchia Ayu ya jaddada matsayinsa na shugaban jam’iyyar tare da cewa babu wanda ya isa ya sauke shi daga muƙaminsa.

Mista Iyorchia Ayu ya yi wannan iƙirarin ne a lokacin da yake ganawa da al’umar ƙabilar Jemgba a gidansa da ke Karamar Hukumar Gboko a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Shugaban Jam’iyyar dai na takun saka da wasu gwamnonin jam’iyyarsa ciki har da gwamnan jiharsa ta Benue Samuel Ortom, wanda ke ta kiraye-kirayen ya sauka daga muƙaminsa.

Ya ƙara tabbatar wa mutanen cewa babu abin da zai sa ya sauka daga mukaminsa.

“Jam’iyyar PDP guda ɗaya ce. Ina bakin ƙoƙari na wajen ganin ban ɓata wa al’umar Benue da na Najeriya ba.

Dan haka idan kun ji suna ta kiraye-kirayen saukeni daga muƙamina, to kar hakan ya dame ku, babu wanda ya isa ya saukeni daga kan kujerar shugabancin jam’iyyarmu. Kawai zan bar kujerar ne ranar da Allah ya kaddara saukata”, in ji Iyorchia Ayu