Wani harin bam ya yi sanadin kashe aƙalla mutum 100 a Somaliya

0
103

Shugaban ƙasar Somalia Hassan Sheikh Mahmud ya tabbatar da cewa aƙalla mutum 100 ne aka kashe sakamakon wasu hare-haren ƙunar baƙin wake biyu da aka kai da motoci a wajen ma’aikatar ilimi ta ƙasar.

BBC ta rawaito cewa; An kai harin ne a jiya Asabar a Mogadishu babban birnin ƙasar. Shugaban ƙasar ya bayyana cewa akwai aƙalla mutum 300 da suka samu raunuka sakamakon wannan harin.

Mista Mahmud ya kai ziyara wurin da aka kai harin inda waɗanda suka shaida lamarin suka bayyana cewa cikin mintoci kaɗan motocin suka ƙaddamar da hare-haren.

Shaidu sun bayyana cewa ita motar ta biyun ma ta kai harin ne a yayin da jama’a suka garzayo da kuma motar ɗaukar marasa lafiya domin kai agaji.

Babu wata ƙunigiya da ta ɗauki nauyin kai harin zuwa yanzu amma ƙungiyar al-Shabab da ke da alaƙa da Al-Qaeda ta sha ƙaddamar da irin waɗannan hare-hare.

Ƙungiyar ta al-Shabab ta yi sanadin mutuwar dubban mutane a ƙasar ta Somalia da kuma rabba miliyoyi da muhallansu.

A ƴan kwanakin nan gwamnatin ƙasar ta rinƙa zafafa hare-hare kan ƴan ƙungiyar, lamarin da ya jawo ita ma ƙungiyar ke zafafa hare-hare.

Ko a kwanakin baya sai da ƙungiyar ta kai hari a wani otel inda ta kashe mutane da dama.