’Yan daba sun kai wa masu zagayen mauludi hari a Neja

0
96

Wasu ’yan daba sun far wa masu zagayen maulidi da mugayen makami, sun hallaka mutum daya, sun ji wa wasu rauni.

Lamarin ya faru ne a Chanchaga ta garin Minna, babban birnin jihar a ranar Asabar.

Waikilinmu ya rawaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:00 na yamma a kusa da Babban Masallacin Juma’a na Chanchaga a inda ’yan daban dauke da makamai suka far wa masu zagayen Maulidin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kara da cewa, mutum hudu sun samu munanan raunuka, an kuma garzaya da su Asibitin Kwararru na IBB.

Sannan ya tabbatar da mutuwar mutum daya.

Kakakin ya ce, rundunar ta tura ’yan sandan sintiri a inda suka cafke mutane shida da ake zargi bayan an same su da miyagun makami, rundunar tana kuma farautar sauran da suka gudu.