Dalilin da yasa na daina rubuta fim ɗin labarina – Ibrahim Birniwa

0
97

Shahararren marubucin fina-finan Kannywood Ibrahim Birniwa ya ce ya daina rubuta fitaccen fim ɗin Labarina mai dogon zango saboda rashin jituwa tsakaninsa da masu shirya shi da kuma aiki kan nasa fim ɗin.

Duk da cewa rashin jituwa ce ta sa marubucin ya fita daga fim ɗin, sai dai ya ƙi faɗa wa BBC Hausa ainahin abin da ya faru, yana mai cewa “da ni nake rubuta fim ɗin da zuwa yanzu ya zo ƙarshe.

Da yake magana ta cikin shirin Amsoshin Takardunku na Sashen Hausa na BBC a ƙarshen mako, Birniwa ya ce ba zai yiwu ya koma rubuta labarin fim ɗin ba a nan gaba saboda wasu dalilai.

Ga masu bibiyar fim ɗin na Labarina, za su lura da daina ganin sunan Ibrahim Birniwa a cikin marubutansa, inda Nasiru Gwangwazo da Yakubu M. Kumo da Saddika Yahaya da Maimuna Beli suka maye gurbin sa.