Rasha ta harba makamai masu linzami fiye da 50 kan Ukraine

0
67

Gwamnatin Ukraine ta ce yankunan kasar da dama ne suka fuskanci hare-haren makamai masu linzami fiye da 50, da dakarun Rasha sunka harba da safiyar wannan Litinin, abin da ya haifar da karin matsalar katsewar wutar lantarki a sassan kasar.

Cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Telegram, rundunar sojin Ukraine ta ce dakarun Rasha sun kaddamar da hare-haren na da misalin karfe 7 na safiyar yau agogon kasar.

Karo na uku kenan da a kasa da watanni biyu sojojin Rasha ke kaddamar da jerin hare-hare da makamai masu linzami kan biranen Ukraine, lamarin da yayi sanadin lalacewar tarin kayayyakin ababen more rayuwa.

A makwannin da suka gabata fadar shugaban Ukraine ta ce gwamman mutane sun rasa rayukansu a sassan kasar, biyo bayan hare-haren makamai masu linzami har sau 190 da Rasha ta kaddamar.

A farkon makon nan, Rasha ta sanar da janyewa daga yarjejeniyar da ke bayar da damar ci gaba da fitar da kayan abinci daga tashoshin jiragen ruwan Ukraine.

Rasha ta ce matakin na ta ya zama dole, saboda yadda ta ce an yi amfani da sararin samaniyar da ke karkashin yarjejeniyar fitar da kayayyakin abincin, wajen kai mata  hari da jiragen yaki marasa matuka.