Ghana ta shirya tsaf don darewa kan kujerar shugabancin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamban wannan shekarar.
Shugabancin wannan kwamitin, wanda wa’adinsa wata guda ne kacal, zai bai wa Ghana damar jan ragamar muhawwarorin da za a yi, wadanda ke da nasaba da zaman lafiya da tsaron duniya.
Ana sa ran shugaban Ghana, Nana Akufo Ado da kuma ministan harkokin wajen kasar su kasance a birnin New York na Amurka don halartar taron.
Kwamitin tsaron yana da mambobi 15 ne,kuma shi ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.