HomeLabarai’Yan bindiga sun sace mutum 6 a wata unguwa a Zariya

’Yan bindiga sun sace mutum 6 a wata unguwa a Zariya

Date:

Related stories

INEC ta ce ba a kammala zabe a jihar Adamawa ba

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta ayyana zaben gwamnan jihar...

An kashe ‘yan sanda 2, da dama sun raunata a wata arangama da sojoji a Taraba

A ranar Litin ne wasu sojoji suka kashe ‘yansanda...

Gwamna Zulum ya sake lashe zaben gwamna a jihar Borno

Sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar...

Sojoji sun kashe hatsabinin dan ta’adda Umaru Nagona

Dakarun sojin Najeriya sun hallaka, Umaru Nagona, daya daga...

An kona gidan mawakin siyasa Rarara a Kano

Wasu da ake zargi ’yan daba ne sun banka...

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari Unguwar Kofar Gayan da ke Karamar Hukumar Zariya inda suka yi awon gaba da mutane shida a ranar Lahadi da daddare.

Wata majiyar jami’an tsaro ta sanar da Aminiya cewa, maharan sun afka Unguwar ce da misalin karfe 11.30 na dare inda suka rika harbe-harbe kafin daga bisani su dauke mutane shidan.

Majiyar ta bayyana wasu daga cikin mutanen da aka dauke sun hada wasu ma’aurata – Khalifa Ibrahim da matarsa Karima Khalifa, da wani malamin addini; Abdulkadir Alaramma, Idris Musa da kuma wani Ikira Isiyaku.

Duk kokarin tuntubar Jami’in rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna Mohammed Jalinge ya ci tura, sakamakon rashin samun wayarsa a lokacin hada wannan rahoto.

’Yan Unguwar Kofar Gayan dai sun dade suna fama da hare-haren ’yan bindiga a ’yan shekarun nan, inda suka rika fuskantar sace-sacen mutane akai akai.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, a unguwar ce aka taba dauke wani jami’in Hukumar Kwastam wanda ya shafe kwanaki 69 a hannun maharan, wanda daga bisani suka sako shi bayan karbar kudin fansa.

Unguwar Kofar Gayan ce dai matsugunar Babban Asibitin Gambo Sawaba da ta kunshi gidaje masu saukin kudi da ake kira Lowcost.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories