Matar da ta kashe mijinta da guba a Borno ta shiga hannu

0
86

Rundunar ‘yan sandan Jihar Borno ta sanar da kama wata matar aure mai kimanin shekara 25 da ake zargi da kashe mijinta ta hanyar sanya masa guba a abinci

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Abdu Umar ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta kama wadda ake zargin ce a ranar 19 ga watan Oktoba a unguwar Doki da ke cikin birnin Maiduguri.

Umar ya ce marigayin wanda shi ne Babban Limamin yankin, ya dawo daga masallaci ne a lokacin da wadda ake zargin – wadda matar sa ce ta aure ta biyu, ta sanya guba a cikin abincinsa.

“Lokacin da marigayin ya fara cin abincini, sai nan da nan yanayinsa ya fara sauyawa.

“Nan take aka garzaya da marigayin zuwa asibitin inda aka ba shi kulawar gaggawa, amma daga baya ya rasu bayan sun dawo gida.

Wannan lamari ya sanya Kwamishinan ‘yan sandan ya tura jami’an binciken laifuka da leken asiri don kamo matar da ake zargin bayan dangin wanda abin ya shafa sun kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na GRA.

Da zuwan ‘yan sandan sun riski dimbin matasan unguwa da suka fusata, suna kokarin kai farmaki gidan matar da ake zargin da nufin daukar doka a hannu, amma ‘yan sanda suka samu nasarar shawo kan lamarin.

Ya kara da cewa, wacce ake zargin a cikin bayaninta, ta amsa laifin da ake zargin ta da shi, inda ta ce ta sayi gubar ce a kasuwar Monday Market a lokacin da ta riga ta yanke shawarar kashe shi.

Kwamishinan ya jaddada cewa, tuni an yi rajistar karar a matsayin kisan kai a gaban Ofishin Daraktan Kararrakin Laifukan Jama’a kafin a gurfanar da ita a kotu.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, wadda ake zargin ta kashe mijin nata ne saboda ta gaji da auren.

Ta ce: “Ban taba son auren ba.  Shi ne mijina na biyu;  Na rabu da mijina na farko saboda na tsani auren.

“Duk lokacin dana farga da cewa na yi aure, abin ya kan bani haushi. A wani lokaci sai na tsere wurin iyayena don neman a raba auren amma kullum sai su mayar da ni, a ce na yi hakuri.

“A wani lokaci, wata biyu bayan na haifi da na, na gudu na tare a cikin wani gini da ba a kammala ba har kusan sati biyu, daga baya na koma gidan mijina.

“Ba wai bai yi min kyau ba, kuma ba rigima muke yi ba.  Mu biyu ne a gidan, ni ce matarsa ​​ta biyu kuma na aure shi tun 2021 amma ni dai ina kyama idan kowane mutum ya zo kusa da ni.

“Ban san ainihin abin da ke damuna ba ko a yanzu da nake magana da kai, ba na jin cewa ni ce na kashe shi,” a cewar ta cikin zubar hawaye.