Buhari ya kalubalanci ‘yansanda a kan matsalar tsaro

0
103

Shugaban Kasa Muhammad Buhari, ya bayyana matsalolin tsaron da suka addabi kasar nan a matsayin babban kalubalen da ke fuskantar rundunar ‘yansandan, yayin da ya bukaci manyan jami’an rundunar da su yi nazari a kan matakan da ya dace su dauka domin kare lafiya da dukiyoyin al’umma.

Yayin da shugaban ke janyo hankalin manyan jami’an ‘yansanda wajen kaucewa goyan bayan wata jam’iyya, ya ce shirin da suka yi ne zai nuna yadda za su tabbatar da ganin an gudanar da zaben shekara mai zuwa cikin lumana.

Buhari, ya ce an kashe makudan kudade wajen samar da tsaro da kuma shirya zabe mai zuwa, saboda haka babu dalilin da zai sa a bari wasu bata gari su hana gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Yayin da yake bude taron manyan hafsoshin ‘yansandan a Jihar Imo, shugaba Buhari ya ce jami’an ‘yansandan ne za su jagoranci samar da tsaron da ake bukata wajen samun nagartaccen zabe, yayin da ya bayyana aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bai wa ‘yansandan goyon bayan da suke bukata tare da kula da ma’aikatan hukumar.

Buhari ya sake jaddada aniyarsa na gudanar da sahihin zaben da duniya za ta amince da shi a shekarar 2023.