Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara ya rasu

0
82

Shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Zamafara, Ahmad Sani Kaura, ya rasu yau Laraba a garin Gusau, babban birnin jihar.

An ruwaito cewa, marigayi Kaura, ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya fadi a yayin wani taro na rattaba hannun yarjeniyar zaman lafiya da cibiyar malamai ta Ulama, reshen jihar da ta shirya don a gudanar da zaben 2023 ba tare da aukuwar wani hargitsin zabe ba.

An ruwaito wani jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Zamafara, Aminu Umar ya sanar cewa, marigayin ya kasance baya jin dadin jikinsa domin bai dade da warkewa daga jinya ba, amma ya halarci taron.