Gwamnati na yunkurin mayar da mu ma’aikatan wucin-gadi – ASUU

0
58

Kungiyar Malaman jami’a ta Najeriya ASUU ta soki gwamnatin tarayya saboda biyan malaman jami’o’in kasar rabin albashin watan Oktoba.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar ta fitar ranar Talata, ya ce kungiyar ta yi Allah wadai irin biyan da gwamnatin tarayyar ta yi mambobinta.

Haka kuma sanarwar ta zargi gwamnatin Tarayya da yunkurin mayar da malaman jami’a ma’aikatan wucin-gadi, wadanda za su yi aiki a biya su nan take.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta biya malaman rabin albashin watan Oktaba, tana mai cewa ba za ta biya malaman kudin aikin da ba su yi ba.

A ranar 14 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai kungiyar ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe wata takwas suna yajin aiki, bayan da kotun ma’aikata ta umarci malaman da su koma bakin aikinsu.