El-Rufai ya bada umarnin dawo wa da iyayen yara kudin makarantar da suka biya

0
110

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya soke biyan kudin makaranta a makarantun sakandaren gwamnati tare da umartar shugabannin makarantu su mayar wa iyayen daliban da suka riga suka biya kudadensu.

Gwamnan ya ce sabon tsarin da Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta kirkira, ya saba wa alkwarin da ya yi al’ummar jihar na ba su ilimin sakandare kyauta, don haka a mayar wa duk wanda ya biya kudin ba tare da bata lokaci ba.

A wani taro da majalisar zartarwar jihar ta gudanar ranar Litinin tare da gwamnan, ta ce tsarin ba da ilimin boko kyauta na shekaru 12 na farko, abin alfaharin gwamnatin ne, don haka za ta ci gaba da aiwatar da shi.

A baya ne dai ma’aiktar ilimin jihar ta ce dole ne daliban sakandaren gwamnatin  su biya kudin makaranta daga yanzu.

Sai dai cikin wata sanarwa da mashawarcin gwamnan kan yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar ranar Talata, ya ce taron ya tattauna yadda za a samar wa ma’aikatar isassun kudaden gudanar da makarantun, ba tare da dalibai sun biya kudin makaranta ba.