Tarayyar Turai ta ware Yuro dubu dari biyar domin yakar cutar kwalara a Najeriya

0
89

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta ce ta ware kimanin Yuro 500,000 domin tallafa wa Najeriya a yakin da take yi da annobar Kwalarar da ta addabi kasarnan.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Laraba ta ce, matakin zai kasance ne musamman ga wadanda abin ya shafa a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

EU ta ce akalla kusan mutum miliyan 1.6 da ’yan gudun hijira miliyan daya ke cikin hatsarin kamuwa da cutar, yayin da akalla mutane 11,820 suka kamu da ita, wasu 382 kuma suka mutu a cikin jihohin uku.

Kwamishiniyar EU mai kula da rikice-rikice, Janez Lenarčič ta ce, “Najeriya na fuskantar rikice-rikice da dama a lokaci guda, ciki har da barkewar cutar kyanda da zazzabin cizon sauro, da karancin abinci da rashin abinci mai gina jiki, da bala’in ambaliyar ruwa – na karshen kuma yana yin illa ga yaduwar cutar kwalara.

“Bugu da kari, yanayin tsaro ya sanya al’ummomi da yawa na kara zama kalubale wadda tare da tallafin EU da abokan aikinmu na jinkai za su yi aiki don rage cututtuka da mace-mace ta hanyar ganowa da wuri, wayar da kan jama’a, ilimin kiwon lafiya da sauran su,” inji ta.

Tuni dai EU ta ware Yuro 100,000 ga Najeriya domin magance ambaliyar ruwan da ta addabi kasar.

Kazalika, a cikin watan Oktoban 2022, EU ta kuma ba da taimakon jinkai na Yuro miliyan 700,000 don tallafa wa yaki da annobar kwalara a Siriya, Yuro miliyan 100,000 don bullar cutar a Habasha da kuma Yuro miliyan daya a Haiti.

Tarayyar Turai da mambobinta na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba a duniya wajen bayar da agajin jinka, musamman dangane da kudirin kungiyar na taimaka wa mabukata a fadin duniya.