Fasinjoji 14 sun kone kurmus a hatsarin mota a Kano – FRSC

0
99

Fasinjoji 14 ne hukumar kiyaye hadura ta kasa, ta tabbatar da konewarsu kurmus a kan hanyar Gaya zuwa Wudil a Jihar Kano sakamakon wani hatsari da ya rutsa da motar bas Toyota Hummer da wata mota kirar Hyundai Jeep.

Zubairu Mato, Kwamandan Hukumar FRSC a Jihar Kano, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata.

Ya ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 7:45 na yamma, kuma jami’an kiyaye hadura sun isa wurin da lamarin ya faru a kauyen Rege da ke unguwar Antukuwani, a kan hanyar Kano zuwa Gaya domin taimakawa wadanda abin ya shafa.

“Da misalin karfe 7:30 na daren Lahadi ne aka yi karo tsakanin wata motar bas mai lamba GML 102 TA Kano daga Jihar Gombe da wata mota kirar Jeep.

“Fasinjoji 13 ne suka kone kurmus nan take tare da jikkata wasu 6 a hadarin.

“Daya daga cikin fasinjojin mace ta rasu a safiyar ranar Litinin a asibitin koyarwa na Aminu Kano.”

Zubairu Mato ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudu mara tushe da kuma wuce gona da iri.

Kwamandan sashen na FRSC ya bukaci direbobi da matafiya da su tabbatar da amfani da na’urorin da suke da iyaka da sauri tare da kaucewa yayin tukin ganganci a kan manyan tituna.