‘Yan sanda sun damke mutane 3 kan zargin sace wata alkali a Ilorin

0
63

Rundunar ‘yansandan Jihar Kwara ta kama wasu mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da wata babbar alkalin kotun majistire a jihar, Misis Jumoke Bamigboye.

A ranar Asabar ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Jumoke Bamigboye, matar tsohon shugaban mulkin soja na jihohin Bauchi da Osun, inda suka saketa a daren Litinin bayan kwashe kwanaki uku a hannunsu.

An sace ta ne a unguwar Oko-Olowo da ke Ilorin, babban birnin jihar, yayin da take dawowa daga gonarta

Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su Naira miliyan 100 domin su sako ta amma daga baya suka yanke rage kudin zuwa Naira miliyan 50 bayan tattaunawa da iyalanta.

Duk da cewa mijin nata, Kanal Theophilus Bamigboye (mai ritaya), ya tabbatar da cewa an biya kudin fansa ga masu garkuwa da mutanen, bai bayyana takamaiman adadin kudin da aka biya na sakin ta ba.

Sai dai ya ce an kai ta asibiti domin kula da lafiyarta bayan an sako ta daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata a Ilorin, ya bayyana cewa an kama wasu mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da ita yayin da ake ci gaba da neman kama sauran wadanda ake zargi da hannu a ciki.