IPMAN na son a yi karin kuɗin fetur a Najeriya

0
120

Kungiyar dillalan man fetur ta kasa a Najeriya, IPMAN, ta bukaci a yi karin kudin man fetur a hukumance muddin ana so a saukaka wahalhalun samun mai da kuma kawo karshen karancinsa.

IPMAN ta yi wannan kira ne a daidai lokacin da ‘yan kasar ke cigaba da fuskantar karancin mai a galibin jihohin arewa da babban birnin tarayya Abuja.

An kwashe ‘yan makonni ana fama da karancin man fetur, duk da irin matakan da gwamnati ke cewa tana ɗauka domin saukaka matsalar.

Kusan tun a farkon wannan shekara zuwa wannan lokaci ba a daukar wani dogon lokaci ba tare da an faɗa cikin karancin fetur ba a Najeriya.