Ana yi wa rayuwata barazana kan sauya fasalin NNPC – Kyari

0
74

Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya ce ana yi masa barazanar kisa sakamakon aikin sauya fasalin kamfanin da yake gudanarwa.

Kyari ya bayyana haka ne a wajen wani taro da Kwamitin Majalisar Wakilai Kan Yaki da Rashawa ya shirya, ranar Laraba a Abuja.

Taron ya mayar da hankali ne kan tattauna batun da ya shafi aiki da gaskiya a fannin mai da makamashin gas har da irin kalubalen da fannin ke fuskanta.

Kyari ya ce, sakamakon dabbaka Dokar Bangaren Man Fetur (PIA), hakan ya haifar da sauye-sauye masu yawa da suka shafi tsare-tsaren kamfanin, sabanin yadda aka sani a baya.

Ya kara da cewa, a halin da ake ciki, kamfanin ya samu nasarar dakile haramtattun matattun mai da dama, wadanda kan haifar da koma-baya ga yawan man da ake samarwa a kasar.

Ya ce sakamakon harkokin haramtattun matatun man, yawan man da ake samarwa kullum ya ragu da ganga 700,000.

Kyari ya ce, duk da barazanar kisa da ake yi musu, wannan bai sa sun damu ba, saboda a cewarsa, sun yi amannar mutum ba ya mutuwa sai idan kwanansa ne ya kare.