Kotu ta bada umurnin tsare shugaban EFCC a gidan yari

0
107

Babbar Kotun tarayya dake Abuja, babban birnin Najeriya ta bada Umarnin tsare shugaban hukumar hana cin hanci da rashawa ta kasar EFCC, Abdurrasheed Bawa a gidan yari sakamakon zargin sa da raina kotu.

Tun farko dai kotun ta zargi Bawa da yin biris da Umarnin da kotun ta bai wa hukumar sa na mayarwa da wani da hukumar ke zargi da cin hanci da rashawa motar sa kirar Range Rover da wasu zunzurutun kudade har Naira miliyan 40.

Yayin zaman kotun na Talata, mai shari’a Chizoba ta yi watsi da hanzarin lauyan EFCC Francis Jirbo wanda ke kokarin kare matakin wanda yake karewa kan dalilin rashin mayar da kadarorin.

Wanda kotun ke bukatar a mayarwa kadorin sa da EFCC ta kwace Rufus Adeniyi Ojuawo tsohon ma’aikaci a Hukumar zirga-zirgar jiragen saman kasar ya sake shigar da karar EFCC na kin biyayya ga hukuncin farko a ranar 28 ga watan October, inda yake bukatar kotun ta yi amfani da karfin ta wajen kwato masa hakkin sa a wajen EFCC.

Tun a shekarar 2016 ne EFCC ta kama Ojowu tare da gurfanar da shi gaban kotu bisa zargin sa karbar rashawar naira miliyan 40 daga wani mai suna Hima Abubakar jami’in wani kamfanimai suna D’Equipment Internationaux Nigeria Limited.