Dattawan Arewa sun yi tir da kai wa Atiku hari a Borno

0
102

Kungiyar tuntuɓa ta dattijan arewa ta yi tir da harin da wasu `yan bangar siyasa suka kai wa kwambar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam`iyyar PDP, a Maiduguri lokacin da yake yaƙin neman zaɓe, a jiya Laraba.

Kungiyar ta yi gargadin cewa irin wannan hari na iya haddasa rikici a ƙasar matuƙar ɓangaren da aka cutar ya nemi yin ramuwar gayya.

Ta dai ja hankalin ‘yan siyasa su dinga taka wa magoya bayansu burki, idan kuma ba haka ba za ta shawarci al’umma su juya musu baya, kamar yada sakataren ƙungiyar Malam Murtala Aliyu ya shaidawa BBC.

A jiya Labara ne dai aka kai harin a lokacin da motocin Atiku ke kan hanya zuwa dandalin taro na Ramat Square da ke birnin na Maiduguri, domin yi wa magoya bayansa jawabi.

Farmakin ya yi sanadiyyar farfasa wasu motocin da ke cikin jerin gwanon, haka nan wasu bayanai na cewa akwai mutane da aka raunata.

Sai dai yan sanda a jihar Borno sun musanta cewar an kai wa ayarin motocin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP hari.

Mai magana da yawun rundunar a jihar Borno, ASP Kamilu Shatambaya lokacin da ya gana da manema labaru, ya ce zargin kai wa ayarin motocin Atiku Abubakar hari shaci-faɗi ne kawai.

Sai dai ya ce an kama wani mutum mai suna Danladi Abbas saboda yunƙurin da ya yi na jifan ayarin motocin ɗan takaran a kan hanyar filin jirgin sama na Maiduguri.