Gwamnatin Kaduna ta karyata rahoton kai hari a hanyar Kaduna – Abuja

0
111

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bukaci al’ummar jihar da masu bin babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da su yi watsi da sakonnin da wasu marasa kishi ke yadawa a Intanet cewar ‘yan bindiga sun kai wani sabon hari.

A cikin sanarwar da Kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya fitar a yau Alhamis, ya ce sakonin karya ne tsagwaronta kuma wasu marasa kishin jihar ne suka kitsa.

Aruwan ya ce gwamnatin jihar a ko da yaushe, tana bibiyar yadda lamarin tsaro ke tafiya a kan babbar hanyar da kuma a sauran gurare da ke a hanyar.

A cewar kwamishinan, gwamnatin jihar na sane da kalubalen rashin tsaron da jihar ke fuskanta kuma tana ci gaba da daukar kwararan matakai domin magance kalubalen.

Aruwan ya kuma nuna takaicinsa a kan yadda wasu za su dinga yada irin wadannan sakonni na karya domin kawai su dakushe kokarin da hukumomin tsaro a jihar ke ci gaba da yi na sadaukar da kai domin a lalubo mafita a kan matsalar.